<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Mun gode maka Yesu, Ɗan Maƙamnacinmu
 Do kana ta lura da mu, ɓatattun tumaki.

[V2]
 KORUS
 Yabo ya tabbata, ya tabbata ga Yesu
 Yesu, Yesu, sunanka da daɗi.
 Karɓi roƙon bayinka domin su sami tsira.

[V3]
 2) A cikin sunan Yesu muna kurkusa ga Allah
 Shi wanda ya mutu domin dukan mutane.
 Korus

[V4]
 3) A cikin yaƙin nan muna da aboka gabanmu.
 Kai ne za ka taimake domin mu ci magabta.
 Korus

[V5]
 4)In na tuna, in na tuna da ƙamnar Almasihu
 Sai hawaye na zuba domin na ɓata hanya.
 Korus</lyrics>
<title>Mun Gode Maka Yesu, Ɗan Maƙamnacinmu LW486</title>
<hymn_number>486</hymn_number>
</song>